image
image

2026 Hasashen Yaneyi

Topic: SCP

Document Type: SCP

NiMet
Download counts 11

Hasashen Yanayi na shekarar 2026 na hukumar (SCP) ya ta'allaka ne kan hasashen raunin La Niña da kuma yanayin tsaka-tsaki na El Niño Southern Oscillation (ENSO). Hasashen ya nuna fara ruwan sama da wuri fiye da yadda aka saba a wasu wurare, farawar ruwan sama a kan lokaci a yawancin sassan ƙasar nan, dakatarwar ruwan sama daga kan lokaci zuwa ƙarshen lokaci, da kuma yawan ruwan sama daga na al'ada zuwa sama da al'ada a mafi yawan sassan ƙasar nan. Ana sa ran yanayin zafi zai kasance sama da al'ada a yawancin sassan ƙasar. Kalmar farawar ruwan sama (onset) na nufin lokacin da ake sa ran ruwan sama zai fara, yayin da dakatarwa (cessation) ke nufin lokacin da ake sa ran zai ƙare. Tsawon kakar ruwan sama kuwa yana nufin tsawon lokacin da ke tsakanin farawa da ƙarewar ruwan saman.

NiMet Weather Assistant

NiMet Weather Assistant

Get expert insights on Seasonal Climate Predictions

Welcome to NiMet Assistant

Ask me anything about Seasonal Climate Predictions or general weather information